Ɗaya daga cikin abubuwan da suka ja hankali a yau bayan bikin ‘yancin kai a Najeriya har da zanga-zangar tsadar rayuwa da wasu matasa suka yi a wasu biranen ƙasar.
Da yake jawabi ga ‘yanƙasa a safiyar yau, Shugaban Ƙasa Bola Tinubu ya ce “ina sane da ƙalubalen da akasarinku ke shan fama da su a irin wannan lokaci”.
A cewarsa: “Gwamnatinmu na sane cewa da yawanku suna fama da hauhawar farashi da kuma neman aikin yi. Ina tabbatar muku an ji koke-kokenku.”
‘Yan mintuna bayan fitowar masu zanga-zangar a yankin Utako na babban birnin ƙasar Abuja ‘yansanda suka fara harba musu barkonon tsohuwa tare da tarwatsa su.
An gudanar da irin wannan zanga-zanga a jihar Legas da ke kudancin ƙasar, sai dai ita ma ba ta yi wani tasiri ba yayin da mutane ke cikin gidaje suna yin hutun Ranar ‘Yanci.


