fidelitybank

Ina jajantawa gwamnan Borno da al’ummarsa – Abiodun

Date:

Shugaban kungiyar gwamnonin Kudu kuma gwamnan jihar Ogun, Prince Dapo Abiodun, ya jajanta wa takwaransa na jihar Borno, Farfesa Babagana Zulum, da al’ummar jihar kan lamarin ambaliyar ruwa da ta afku a Maiduguri, babban birnin jihar kwanan nan.

Gwamnan, a wata sanarwa mai dauke da sa hannun mai ba shi shawara na musamman kan harkokin yada labarai da dabaru, Hon. Kayode Akinmade, ya ce ambaliyar ruwan ta haifar da munanan matsalolin jin kai a jihar, wanda ke bukatar tallafin gaggawa daga dukkan ‘yan Najeriya masu kishin kasa.

Ya ce, “yayin da bala’o’in da ke faruwa a wannan yanayi ba su da makawa, daukar matakin gaggawa irin na gwamnatin Borno da na gwamnatin tarayya zai taimaka matuka wajen daidaita lamarin da kuma kawo dauki ga jama’a cikin gaggawa.”

“Ina mika ta’aziyya ga dan uwana Farfesa Babagana Zulum da al’ummar Jihar Borno bisa mummunar ambaliyar ruwa da ta afku a Jihar, wanda ya haifar da matsalar jin kai mai girman gaske.

“Gwamnati da al’ummar jihar Ogun na tare da Borno a wannan lokaci na kunci kuma za mu ci gaba da yi musu addu’a,” in ji sanarwar.

taraba news

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp