fidelitybank

Ina jajanta wa mutanen da suka mutu a Kano – Buhari

Date:

Shugaban kasa, Muhammadu Buhari, ya jajanta wa iyalan mutanen da suka yi asarar rayuka a Sabon Gari, Kano, sakamakon fashewar tukunyar iskar gas a ranar Talata, inda aka samu asarar rayuka tara, ya kuma umurci jami’ai da su ba da isassun magunguna ga wadanda suka jikkata.

“Fashewar tukunyar iskar gas a Kano abin bakin ciki ne. Ina mika ta’aziyyata ga iyalan wadanda suka rasa rayukansu. Ina yi wa wadanda suka jikkata fatan samun sauki cikin gaggawa,” in ji shugaban, a cewar wata sanarwar manema labarai da kakakinsa Garba Shehu ya fitar.

Ya kara da cewa, “A wannan lokaci na bakin ciki, ina rokon Allah Madaukakin Sarki da Ya karawa iyalan wadanda abin ya shafa juriya, gwamnati da al’ummar Jihar Kano tare da rokonsu da su dauki nauyin wannan rashi da ba za a iya kwatantawa ba.”

Shugaba Buhari ya yaba da matakin gaggawa da hukumomin gwamnatin jihar, da hukumar bada agajin gaggawa ta NEMA, da sojoji, da ‘yan sanda da sauran hukumomin gwamnatin tarayya.

today daily post news

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp