A ranar Lahadin nan ne shugaban kasa Bola Tinubu, ya jajantawa al’umma da gwamnatin jihar Zamfara kan ambaliyar ruwa da ta afku a karamar hukumar Gummi da kuma mutuwar manoma sama da 40 a wani hatsarin kwale-kwale a karshen mako.
Bayo Onanuga, mai baiwa shugaban kasa shawara kan yada labarai da dabaru ne ya bayyana hakan a wata sanarwa.
Sanarwar ta ce, Tinubu ya yi alkawarin tallafa wa wadanda abin ya shafa da suka rutsa da su.
“Shugaban ya umurci hukumomin gaggawa da su yi cikakken nazari kan al’amuran biyu don magance tushen bala’in.
“Shugaba Tinubu ya kuma umurci hukumomin mayar da martani da su hada kai da gwamnatin jihar Zamfara domin taimakawa wadanda bala’in ya shafa,” in ji sanarwar.