A ranar Talata ne Shugaba Bola Tinubu ya jajanta wa kungiyar Tijjaniyya a Najeriya, bisa rasuwar mambobinta 40 da suka mutu a wani hadarin mota da ya rutsa da su a ranar Lahadi.
An jikkata wasu da dama a lamarin.
Mutanen da lamarin ya rutsa da su sun fito ne daga Kwandari a Filato bayan bikin Mauludi a garin Saminaka na jihar Kaduna, inda motar bas din su ta yi karo da wata babbar mota a Lere, Kaduna.
Shugaba Tinubu ya jajantawa iyalan wadanda lamarin ya rutsa da su da kuma gwamnatocin jihohin Kaduna da Filato, Mista Bayo Onanuga, mai baiwa shugaban kasa shawara kan harkokin yada labarai da dabaru ya bayyana a cikin wata sanarwa.
Ya yi addu’ar Allah ya jikan wadanda suka rasu.
Shugaban ya umurci hukumar kiyaye haddura ta kasa FRSC da ta inganta hanyoyin sa ido da kuma rage yawan hadurran tituna a fadin kasar nan.