Tsohon shugaban ƙasar Amurka, Barack Obama, ya nuna goyon baya ga mataimakiyar shugaban ƙasar, Kamala Harris a matsayin ƴar takarar shugaban ƙasa a jam’iyyar Democrat.
Cikin wata sanarwar haɗin gwiwa tare da mai ɗakinsa Michelle Obama, sun yaba wa Ms Harris kan “hangen nesanta da kyawawan ɗabi’unta, da kuma ƙwarin gwiwar da ake buƙata a wannan lokaci da suka bayyana da ”mawuyaci”.
Rahotonni sun ce Mista Obama na cikin fitattun ‘yan jam’iyyar Democrat fiye da 100, da Harris ta tuntuɓa bayan Shugaba Biden ya sanar da janyewa daga takarar a ranar Lahadin da ta gabata.
Harris ta sami goyon bayan akasarin wakilan da za suyi zaɓen fitar da ɗan takara, da za a yi a babban taron jam’iyyar a watan Agusta.


