Biodun Oyebanji zababben gwamnan jihar Ekiti, ya godewa masu kada kuri’a da suka bashi gagarumar nasara a ranar Asabar.
A wani sako da ya wallafa a Facebook, Oyebanji ya nuna godiyarsa.
A sauƙaƙe ya rubuta: “Na gode Ekiti Kete”
Bugu da kari, ya saka hoton nasa a wajen gangamin yakin neman zaben ranar Talata a Ado-Ekiti, yana rike da tsintsiya madaurinki daya.
Oyebanji, wanda dan takarar gwamna mai barin gado, Kayode Fayemi, ya samu kuri’u 187,057 inda ya kayar da babban abokin hamayyarsa, Segun Oni na jam’iyyar Social Democratic Party, wanda ya samu kuri’u 82,211.