Tsohon suaban Amurka Joe Biden, ya miƙa godiyarsa ga masoyansa da waɗanda suka yi masa fata ta gari bayan an bayyana ya kamu da cutar kansar ƙasan mafitsara.
A wani saƙon da ya wallafa a kafar X, Mista Biden ya ce kamuwa da ya yi da cutar kansar ya shafi kow, inda ya godewa mutane da suka nuna damuwar su da yi masa fatan samun lafiya.
Manyan ‘yan jam’iyyar Democracts da Republican sikin su har da wanda ya gaje shi shugaba Donald Trump duka sun yi ma tshon shugaban na Amurka mai shekara tamanin da biyu adu’a.
Bayanan lafiyar shugaban da aka fiyar dai sun ce cutar ta yaɗu zuwa ƙasusuwansa, sa dai likitocinsa sun ce ana ci gaba da duba lafiyarsa.