Kocin Norway, Stale Solbakken, ya caccaki tsohon kocin Arsenal Arsene Wenger, yana mai cewa FIFA ta sauya masa tinani.
Wannan dai na zuwa ne bayan da Bafaranshen ya bayyana a kwanan baya cewa zanga-zangar da Jamus ta yi a gasar cin kofin duniya na nuna rashin amincewa da batun kare hakkin bil’adama a Qatar ne ke da alhakin ficewarsu da wuri.
A cewar Solbakken, fitaccen mai horaswar an wanke kwakwalwarsa daga hukumar FIFA inda yake aiki tun bayan barin aiki a Emirates.
Dan shekaru 73 da haifuwa ya yi nuni da cewa fafatawar da Jamus ta yi a matakin rukuni-rukuni na gasar cin kofin duniya da aka yi a Qatar ya faru ne sakamakon zanga-zangar siyasa da suka yi kafin su kayar da Japan.
Da yake magana da tashar talabijin ta Norway ta TV 2, Solbakken ya ce: “[Wenger] ko ta yaya an goge masa kwakwalwa kuma yanzu yana yin maganganun wauta.
“Yana da ban tsoro ga duk mutanen da muka yi tsammani a duniyar kwallon kafa tsawon shekaru.
“Akwai rikice-rikice da ke faruwa a yanzu, kuma ina jin tsoron zai yi muni.”