Tsohon Gwamna kuma Sanata mai wakiltar mazabar Imo ta Yamma, Rochas Okorocha, ya yi magana a karon farko tun bayan kada kuri’u a zaben fidda gwani na shugaban kasa na jam’iyyar All Progressives Congress (APC) a ranar Talata.
An dai samu firgici a wasu sassan cewa tsohon gwamnan jihar Imo na iya ficewa daga jam’iyyar bayan ya kasa cin tikitin takara.
Sai dai kuma, tsohon gwamnan a wata sanarwa da mai baiwa ‘yan jaridu shawara ta musamman kan harkokin yada labarai, Sam Onwuemeodo ya rabawa manema labarai a ranar Juma’a, ya ce Okorocha na fatan Asiwaju ya samu nasara yayin da ya daga tutar jam’iyyar APC a zaben 2023.
Okorocha ya ce, “Ina yaba wa duk wadanda suka halarci zaben fidda gwani na jam’iyyar APC domin samun tikitin takarar shugaban kasa.
Okorocha ya ce, “Ina taya Asiwaju Bola Tinubu murna, bisa nasarar da ya samu a zaben fidda gwani na shugaban kasa na jam’iyyar All Progressives Congress, APC.