Shugaban kasa Muhammadu Buhari, ya ce yana fatan ganin an gudanar da zaben 2023 cikin kwanciyar hankali yayin da gwamnatinsa ke tafiyar da mulkin kasar sannu a hankali.
Yayin da za a gudanar da zaben shugaban kasa da na ‘yan majalisun tarayya a ranar 25 ga Fabrairu, 2023, na gwamnoni da na majalisun jihohi kuma za a yi zaben ranar 11 ga Maris na shekara mai zuwa.
Da yake jawabi a lokacin bikin Sallah ga Sarkin Katsina, Abdulmumini Kabir Usman a fadarsa da ke Katsina, Shugaban ya yi alkawarin magance matsalolin tsaro da kasar nan ke fuskanta.
Ya kuma yi alkawarin gyara wasu sassan tattalin arziki kafin kammala mulkin sa a ranar 29 ga Mayu, 2023.