Dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar PDP, Atiku Abubakar, ya yi tsokaci kan kara hadin gwiwa tsakanin gwamnatin Birtaniya da Najeriya, wajen lalubo hanyoyin da za a magance matsalolin da ke da amfani ga kasashen biyu.
Atiku, ya bayar da shawarar ne a lokacin da tawagar babbar hukumar Burtaniya karkashin jagorancin High Catriona Laing ta gana da Atiku a gidansa da ke Abuja a jiya.
A yayin ganawar Atiku da bakinsa sun tattauna batutuwa da dama da suka shafi tsaro, ilimi, noma, tattalin arziki da kuma samar da hadin kan kasa a Najeriya.
Babban Kwamishinan ya bayyana cewa, ganawar da tsohon mataimakin shugaban kasar wani bangare ne na ci gaba da gudanar da ayyukan gwamnatin Burtaniya, domin inganta dimokuradiyya da sahihin zabe a Najeriya.
Da yake mayar da martani, Atiku ya nuna jin dadinsa ga tawagar da suka ba da lokacin gudanar da taron, ya kuma bayyana cewa, “dangantakar da ke tsakanin Najeriya da Birtaniya na da tarihi mai dimbin yawa, kuma yana da muhimmanci kasashen biyu su yi amfani da wannan damar wajen inganta al’amuran da suka shafi kasashen biyu tare da damuwa da juna.”
Wazirin Adamawa ya jaddada cewa, yana sa ran kasar Ingila za ta taka rawar gani wajen tabbatar da dorewar dimokuradiyya a Najeriya, kuma yana da yakinin cewa, zaben shugaban kasa a 2023 zai kasance cikin gaskiya da adalci.
A kan batun rashin tsaro, ya yi tir da halin da ake ciki a kasar, ya kuma nemi taimakon Birtaniya musamman a fannin horarwa da musayar bayanan sirri.
Da yake magana game da tattalin arziki, tsohon mataimakin shugaban kasar ya ce, idan aka ba shi dama ya jagoranci al’amuran Najeriya, zai tare da sauran abubuwa, zai kawar da tsarin musayar kudade da yawa tare da rage haraji don karfafa masana’antu na gaske da kuma bunkasa jari na gaske. Ya kuma yi alkawarin bunkasa harkar noma, domin samar da ayyukan yi ga al’ummar kasar nan.
Bugu da kari, dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar PDP ya bayyana damuwarsa kan yajin aikin da kungiyar malaman jami’o’i ke yi da kuma rikicin da ke faruwa a fannin ilimi.
Ya yi alkawarin aiwatar da gyare-gyare a fannin ilimi, gami da sake farfado da shirin ba da lamuni na kudi ga daliban Najeriya.


