Shugaba Biden ya ce ya yi farin ciki da jin cewa abokin hamayyarsa Donald Trump yana cikin koshin lafiya.
A wani jawabi da ya yi ba shiri ta gidan telebijin a mahafarsa Delaware, ya yi allawadai da lamarin, yana mai bayyana shi a matsayin abun takaici.
Ya ce ”wannan na ɗaya daga cikin dalilan da suka sa wajibi ne mu haɗa kan ƙasar nan, ba za mu ci gaba da tafiya a haka ba, wannan yaƙin neman zaɓe ne da yake da ƴancin yi ba tare da kowacce irin matsala ba.”
Daga baya fadar White House ta tabbatar da cewa Mista Biden ya yi magana da Trump ta waya.
Suma tsofaffin shugabannin ƙasar biyu, Barack Obama da George Bush, sun bayyana jin dadinsu da cewa Mista Trump bai ji rauni sosai ba.
Kwamitin yaƙin neman zaben Mista Trump ya ce duk da harbin da aka yi, babban taron jam’iyyar Republican na wannan makon don tabbatar shi a matsayin dan takara zai gudana, kuma Mista Trump zai halarci taron.


