Sakataren Harkokin Wajen Amurka, Antony Blinken, ya ce ya na da yaƙinin ƙasar Ukraine za ta yi nasara a yakin da suke gwabzawa da Rasha.
Mista Blinken ya ce, ba zai fadi yadda hakan ko tsahon lokacin da za a ɗauka a na yakin tsakanin kasashen biyu ba, sai dai ya yi watsi da batun Rasha ka iya cimma burinta a kan mutum miliyan 45 da ke yakin kwatar ‘yancinsu.
Blinken ya bayyana haka ne a Brussels a kan hanyarsa ta zuwa kasar Poland.
Wakiliyar BBC ta ce a na sa ran da zarar sakataren harkokin wajen ya isa Poland zai kai wa ‘yan gudun hijirar Ukraine ziyara da kara jaddada goyon baya ga kasar.
Sai dai firaministan Poland ya ce, ya na fargabar kar Rasha ta kai hari wajen.