Kwamitin tantance shugaban kasa na jam’iyyar All Progressives Congress (APC) ya tantance mataimakin shugaban kasa Yemi Osinbajo.
Bayan tantancewar, Osinbajo, ya zanta da ‘yan jarida, inda ya ce, tantacewar ya yi tasiri tare da bayyana kwarin guiwar jam’iyyar gabanin zaben shugaban kasa na 2023.
“Mun samu damar tattaunawa kan batutuwa da dama, batutuwan da suka shafi kasa da jam’iyya, kuma abin ya tafi sosai; mun yi hira sosai. Tabbas muna gaban kowace jam’iyya; a gaba, APC na gaba,” inji shi.
Kwamitin da John Odigie-Oyegun ke jagoranta, wanda ya fara aiki a ranar Litinin, zai tantance mutane 25 masu neman tikitin takarar shugaban kasa na jam’iyyar APC da ke neman tikitin jam’iyyar.