Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya ce yana bukatar karin lokaci domin tuntubar juna kan adadin da ya dace a biya a matsayin sabon mafi karancin albashin ma’aikata a ma’aikatun gwamnati.
Shugaban ya bayyana haka ne a taron majalisar zartarwa ta tarayya a ranar Talata, lokacin da aka gabatar da batun domin tattaunawa.
Ministan yada labarai da wayar da kan jama’a na kasa, Mohammed Idris ne ya bayyana hakan a ranar Talata, yayin da yake zantawa da manema labarai na fadar gwamnati.
Ya ce an ajiye takardar ne saboda Gwamnatin Tarayya tana ganin ya dace ta tuntubi sauran masu ruwa da tsaki, musamman ganin yadda sabon tsarin albashin ya shafi kananan hukumomi da jihohi da kuma gwamnatin tarayya.
Ministan ya ce, “Mutane da yawa sun yi ta yi mani tambayoyi kan ko sabon mafi karancin albashin zai zo don tattaunawa a yau a FEC, musamman ko gwamnati za ta samu matsayi kan sabon albashin.
“Ku tuna cewa akwai rahoto daga kwamitin uku, wanda ya hada da kungiyar kwadago ta Najeriya da kungiyar kwadago ta kasa, kungiyoyi masu zaman kansu da kuma wakilan gwamnati, wadannan ukun ne kwamitin bangarorin uku da suka tattauna kan sabon mafi karancin albashi. Sun mika wa shugaban kasa rahoton da ya wuce.
“Amma bisa yadda ya kamata a yi, ina so in sanar da ’yan Najeriya cewa FEC ta tattauna kan hakan saboda sabon mafi karancin albashi na kasa ba wai shawarar gwamnatin tarayya ce kawai ba.
“An ajiye wannan bayanin ne domin baiwa Shugaban kasa damar kara tuntuba domin ya samu cikakken bayani kan abin da zai yi. An dauki wannan matakin ne saboda ya shafi Jihohi, LG da Gwamnatin Tarayya.”