Sanata Mohammed Ali Ndume ya nuna nadama tare da bayar da hakuri kan sukar da ya fito fili ya yi a kan jam’iyyar APC mai mulki a Najeriya da kuma kasar Bola Ahmed Tinubu.
Sai dai a hirarsa da BBC, Sanatan ya ce sun nemi afuwar juna ne shi da jam’iyyarsa ta APC wadda ta ba da umarnin cire shi daga mukamin mai tsawatarwa a majalisar dattawa a watan jiya.
Ndume ya ce sun yi wata ganawa a jiya Talata da shugabannin jam’iyyar kuma ya nemi afuwa game da kalaman sukar da ya yi a kafafen yada labarai maimakon gabatar da koken nasa ga jam’iyyar.
Ya ce shi ma an ba shi hakuri kan abin da aka yi mishi ba tare da an gayyace shi ba, domin ji daga wajenshi.
Sai dai kuma Sanatan mai wakiltar Borno ta Kudu, ya ce har yanzu yana nan kan bakansa na magnaganun da ya yi domin magana ce da ya yi ta gaskiya, kuma saboda kishin kasa ba don wani abu na daban ba.
Sanatan ya ce akwai jam’iyyu kamar PDP ta SDP da wasu da suka fara zawarcinsa domin ya koma can domin ya yi musu takara a zaben 2027, saboda a cewarsa sun ga ba a mishi adalci ba dangane da abin da aka yi masa a APC.
To amma ya ce ai, ”mutum ba zai bar gidansa ya tafi wani waje ba.”
Dangane da tsohon mukamin nasa kuwa an ruwaito shugaban jami’iyyar ta APC Abdullahi Umar Ganduje na cewa za su rubuta wa majalisar dattawa kan ta sake duba maganar ta Ndume da nufin mayar masa da mukamin idan ta ga hakan zai yiwu.


