Wata ƴar Najeriya da ke yi wa ƙasa hidima (NYSC) a birnin Legas, wadda bidiyon ta ya karaɗe shafukan sada zumunta inda ta soki gwamnatin Tinubu kuma ta bayyana Legas a matsayin ‘jiha mai wari’, ta fito fili ta bada haƙuri kan kalaman nata na ƙasƙanci kan Legas.
A shafinta na Instagram, ƴar bautar ƙasar ta amince cewa mai yiwuwa kalamanta ba su yi wa mazauna jihar daɗi ba, kuma ta bayyana nadamarta kan amfani da kalaman.
Ta bayyana cewa ba ta yi niyyar zagin ƴan jihar ba, sai dai kawai tana bayyana abin da ta lura da shi ne a matsayinta na baƙuwa.
Ta kuma ce kalaman nata wani yunkuri ne na fito da matsalolin Najeriya kullun na tsawon kwanaki 30 a jere domin fargar da alumma ke da ita kan matsalolin da ke addabar ƙasar kamar taɓarɓarewar tattalin arziƙi.