Tsohon shugaban ƙungiyar Hamas ya ce, yana alfahari da harin da mayaƙan Hamas suka kai Isra’ila a makon da ya gabata, yana mai cewa harin “yunƙuri ne na kawo ƙarshen mamayar Isra’ila”.
Yayin da yake magana gidan talbijin na Haberturk TV, shugaban hulda da ƙasashen ƙetare na ƙungiyar Hamas, Khalid Meshal ya ce rikici tsakanin Irsa’ila da Falasɗinu ya samo asali ne tun shekarar 1948, ba makon jiya ba.
“Isra’ila na cewa tana da ƙarfin soji, suna cewa ba za a ci galaba a kansu ba. Amma mun yi mamakin yadda aka ci galaba a kansu a makon da ya gabata,” in ji shi.
Da aka tambaye shi game da yadda mayaƙan Hamas ke kai wa fararen hula da ƙananan yara da tsofaffi hari, sai ya ce “Muna faɗa wa mayaƙanmu ka da su yi haka. To amma a lokutan yaƙi irin wadannan ala’umar kan faru. Ba wai yadda Isra’ila ke faɗa a koyaushe cewa ba ta kashe fararen hula”.
Da aka tambaye shi ko Hamas na aikata irin abin da take zargin Isra’ila da aikatawa? Mista Meshal ya ce “akwai babban bambanci”.
“Wannan ƙasarmu ce. Idan maƙiya suka zo daga waje, ko sojoji ko fararen hula, duk dai maƙiya ne, duk wanda ya zo ƙasarmu domin mamaya maƙiyinmu ne, kuma mai laifi”.