fidelitybank

IMF ya roki CBN ya sakarwa ‘yan Najeriya mara

Date:

Asusun bayar da lamuni na duniya, IMF, ya bukaci babban bankin Najeriya da kuma gwamnatin kasar da su kara tsawon wa’adin daina amfani da tsofaffin kudin da aka sauya.

Hukumar ta IMF, ta yi kiran ne ‘yan sa’o’i bayan da Kotun Kolin Najeriya ta yanke hukuncin jingine wa’adin daina amfani da kudin na ranar 10 ga watan Fabrairu, har zuwa lokacin da za ta yi hukunci na karshe a ranar 15 ga watn na Fabrairu.

A wata sanarwa da asusun na IMF ya fitar yau Laraba, mai dauke da sa hannun wata jami’a, Laraba Bonet, ya ce ya yi kiran ne domin wahalar da ‘yan Najeriya suke sha.

Karanta Wannan: Da Dumi-Dumi: Kotu ta dakatar da CBN daga wa’adin karbar tsofaffin kudi

Sanarwar ta ce saboda irin wahalar da jama’a ke sha a harkokin kasuwancinsu da rayuwar yau da kullum saboda karancin sababbin takardun kudin na naira 1,000 da 500 da kuma 200, duk da matakan da Babban Bankin ya dauka, ya kamata hukumomin kasar su sauya shawara.

Hukumar IMF, ita ce ta farko cikin manyan hukumomin kudi na duniya da ta fito fili ta yi kiran tsawaita wa’adin daina amfani da tsofaffin kudin na naira.

mmm.nnn.

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp