Mataimakin shugaban kasa Kashim Shettima ya ce ilimi da bunkasar sana’o’i ne mafita ga yunwa da fatara a Najeriya.
Ya bayyana hakan ne a wani taro da wata kungiya daga gidauniyar Bill & Melinda Gates a ranar Laraba a fadar shugaban kasa da ke Abuja.
Mista Rodger Voorhies, Shugaban Sashin Ci gaban Duniya da Dama na Gidauniyar ne ya jagoranci tafiyar.
Mataimakin shugaban kasa Shettima ya jaddada yadda sauyin yanayi ke shafar amfanin noma da kuma yadda yake da matukar muhimmanci wajen aiwatar da hanyoyin noman da suka dace domin tabbatar da wadatar abinci ga al’ummar Najeriya da ke kara fadada.
Don haka mataimakin shugaban kasar, ya roki gidauniyar Bill & Melinda Gates da ta kulla kawance tare da gwamnatin Najeriya domin bunkasa noman kasar, da inganta abinci mai gina jiki, da kuma karfafa tsarin ilimi.
Ya dorawa gidauniyar taimakawa ayyukan shugaban kasa Bola Tinubu da suka shafi karfafa jinsi, inda ya jaddada mahimmancin shirye-shirye da ya shafi yara mata ga kokarin Najeriya na rage talauci.
Mataimakin shugaban kasa Shettima ya mika godiyarsa kan irin gudunmawar da gidauniyar ke bayarwa a Najeriya, musamman a fannin kiwon lafiya a matakin farko da kuma kawar da cutar shan inna.
“Muna saka hannun jari sosai a kan sabbin hanyoyin noma da kuma mafi kyawun ayyukan noma don haɓaka yawan aiki.
“Duk da haka, muna buƙatar ƙwarewa da albarkatun gidauniyar Bill & Melinda Gates don haɓaka ci gabanmu,” in ji shi.


