fidelitybank

Ilimi: Iyaye ku tura ‘ya’yan ku makarantun Islamiyya – Fa’izu Alfindki

Date:

Shugaban karamar hukumar birni da kewaye, Fa’izu Alfindiki, ya ziyarci makarantar Islamiyya dake Marmara, Kamaluddem Nama’aji Alfindiki School, wacce ta yi nasarar yaye dalibai 90 masu karatun Al-Qur’ani Maza da Mata.

Shugaban karamar hukumar Faizu Alfindiki, ya yabawa mahukuntan makarantar da iyaye bisa yadda suke sadaukar da lokacinsu da dukiyoyinsu wajen jawo ‘ya’yansu, domin samun ilimin addinin musulunci.

Ya ce “Ya na da matukar muhimmanci ba yara kadai ba, har ma da manya su ba da lokacinsu, domin samun ilimin addinin Musulunci, wanda zai samar da zaman lafiya a tsakanin al’umma”. Inji shi

Shugaban karamar hukumar ya kuma yi kira ga iyaye da su tura ‘ya’yansu maza zuwa makarantar Islamiyya, ya na mai cewa abin takaici ne yadda akasarin daliban da suka yaye mata ne. Domin haka ya bukaci daliban da aka yaye da su ci gaba da yin biyayya ga iyayensu, tare da ba da lokacinsu wajen karatun Alkur’ani mai girma a kowane lokaci domin matasa su yi koyi da su.

Fa’izu Alfindiki ya kuma bayyana siyawa makarantar katafaren gida mai hawa biyu a dai-dai lokacin da makarantar ke cikin matsi na rashin isashshen wurin zaman dalibai.

Mai martaba sarkin Kano, Alhaji Aminu Ado Bayero wanda ya jagorancin bikin yaye daliban, ya kuma yi kira ga daukacin malamai na addinin musulunci da limamai da su ba da lokacinsu wajen yi wa kasa addu’ar zaman lafiya.

the sun news

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp