fidelitybank

Ilimi: Dalibin Kano ya yi fintinkau a kasar Indiya

Date:

Wani dalibi dan jihar Kano da ke karatu a kasar Indiya, Abdulrazaq Nafiu Abubakar, mai shekaru 27, ya samu lambar yabo ta Vice Chancellor’s Gold Medal Award a kasar Indiya bayan da ya kammala karatunsa na farko a matsayin dalibin da ya fi kowa kwarewa a fannin fasaha a fannin Injiniya a Jami’ar Sharda ta kasar Indiya.

Abubakar daga karamar hukumar Nasarawa, wanda ya kamala karatun digiri na biyu da maki na CGPA 9.89 cikin 10.00 a kasar Indiya, ya karanta Mechatronics Engineering a Jami’ar Bayero ta Kano a lokacin da ya ke karatun digirinsa na farko, inda ya samu kyautar Ahmadu Adamu Muazu na 2019 a matsayin wanda ya fi kowa samun maki da CGPA 4.9 a tsangaya na Injiniya.

Bayan kammala karatunsa a shekarar 2019, matashin wanda ya kammala karatunsa ya samu gurbin karatu a kasashen waje ga dalibai 370 da suka kammala karatun digiri na farko a Kano, zuwa kasar Indiya domin samun digirinsa na biyu na Master’s na gidauniyar Kwankwasiyya.

Da a ka tambaye shi ta ya ya ya samu wannan nasara, sai ya ce”Duk abin yabo ya tabbata ga masu ba shi shawara wadanda su ka zaburar da shi tare da yi masa jagora har ya kai ga taron.

“To, babu abin da za a ce a kan yadda na fito a matsayin mafi kyawun ɗalibi, nufin Allah ne.

“Amma na san cewa na mai da hankali sosai a duk azuzuwan ilimi na, da kuma dakunan gwaje-gwaje,” in ji shi.

Ya kuma bayyana cewa mafi yawan lokutan hutun sa ya na amfani da su ne wajen ayyuka da bincike, domin ya na da sha’awar koyon kere-keren fasahar zamani.

Nafi’u ya kuma yi nuni da cewa, daya daga cikin manyan kalubalen da ya fuskanta a lokacin da ya ke karatun digiri na farko shi ne wahalar samun bincike a fannin karatunsa, domin wani sabon shiri ne a lokacin.

Yayin tattaunawar sa da DailyTrust, ya bayyana karatu a Indiya a matsayin wani sabon al’amari wanda ya samu damar koyo daban-daban, amma ya kara da cewa, yin karatu a cikin sabon yanayi da kuma lokacin COVID-19 ya na da kalubale, kuma ya na da wahalar jurewa.

labaran duniya na yau

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp