Mata da dama sun fito zanga-zanga, domin adawa da matakin gwamnatin Taliban na rufe makarantun sakandare na mata.
Matan sun fito rike da kwalaye da ke dauke da bayanin cewa “Ilimi ƴancinmu ne, ba tsarin siyasa ba.”
Sai dai rahotanni sun matan sun watse lokacin da sojojin Taliban suka tunkari wurin da suke zanga-zangar.
Wannan ne karon farko da mata suka fito zanga-zanga a Kabul, makwanni bayan Taliban ta kama mata da dama masu fafutikar kare haƙƙin mata.