Bayan kwana biyu da sakin Injiniya Mu’azu Magaji, tsohon kwamishinan Ganduje, ya ziyarci Sanata Ibrahim Shekarau a gidansa da ke Kano.
Kamar yadda Dan Sarauniya ya sanar da manema labarai, ya ce, wannan abu da ya faru da shi karin karfin gwiwa ne na gwagwarmaya.
Ya bayyana cewa, biyayyarsa ta koma ga tsagin Shekarau tunda ya gano cewa, su ke da nufi nagari ga Kanawa da siyasar kasar nan.
Jaridar Daily Trust ta rawaito cewa, Magaji ya gana da Sha’aban Sharada, Danzago da wasu jiga-jigan jam’iyyar.