Kocin Super Eagles, Jose Peseiro, ya ce a yanzu Kelechi Iheanacho ya samu cikakkiyar koshin lafiya don taka leda a gasar cin kofin Afirka na 2023, AFCON, a Cote d’Ivoire.
Paseiro ya bayyana hakan ne a wata hira da ya yi da manema labarai a birnin Abu Dhabi na Hadaddiyar Daular Larabawa da yammacin jiya Litinin.
“Kelechi zai kasance tare da mu a Cote d’Ivoire. Ya gama jinyarsa a Leicester City,” inji shi.
A cewarsa, yanzu Iheanacho zai shiga cikin sauran ‘yan wasan Super Eagles a gasar AFCON bayan ya kammala jinyar raunin da ya samu a tsoka.
Iheanacho ya yi jinya saboda rauni kuma baya cikin atisayen kungiyar na tsawon mako guda a Abu Dhabi.
Dan wasan na Leicester City ya zauna a kulob dinsa domin ya murmure sosai a gasar AFCON da za a fara ranar Asabar a Abidjan na kasar Cote d’Ivoire.
A ranar Laraba ne ake sa ran Super Eagles wadda ta lashe kofin sau uku za ta tashi zuwa kasar Cote d’Ivoire domin halartar gasar cin kofin AFCON karo na 34 bayan halartar liyafar cin abinci ta musamman da Gwamna Babajide Sanwo-Olu zai shirya a Legas ranar Talata (yau).
A ranar 11 ga watan Fabrairu ne za a fara gasar AFCON na tsawon wata guda, inda ake sa ran Super Eagles za su fara fafatawar da Equatorial Guinea a filin wasa na Alassane Ouattara da ke Abidjan.


