Kelechi Iheanacho ya taimaka a wasansa na farko a gasar Premier yayin da Leicester City ta sha kashi a hannun Arsenal da ci 4-2 a filin wasa na Emirates.
Iheanacho ya maye gurbin Jamie Vardy saura minti 20 a tashi daga wasan.
Dan wasan gaba ya zura kwallo ta biyu a ragar Leicester City James Maddison a minti na 74 da fara wasa.
Dan wasan na Najeriya ya kusa kai hari minti biyu da suka wuce.
Abokin wasan Iheanacho na kasa da kasa, Wilfred Ndidi ya buga minti 90 a wasan.
Gabriel Jesus ya zira kwallaye biyu tare da Granit Xhaka da Gabriel Martinelli suma suka ci wa Gunners din.
Har yanzu Leicester City ba ta samu nasara ba a gasar Premier ta bana bayan da suka tashi 2-2 da Brentford a wasansu na farko.


