Mai rajin kare ƙabilar Yarbawa a Najeriya, Oloye Sunday Adeyemo, wanda aka fi sani da Sunday Igboho ya kai ƙara gaban Firaiminisan Birtaniya, Keir Starmer, domin neman taimakonsa wajen kafa ƙasar Yarabawa.
Mai magana da yawun Sunday Igboho, Olayomi Koiki, shi ya bayyana haka a wani sako da ya wallafa a shafinsa na X a yau Lahadi.
Ya ce Igboho ya gabatar da ƙarar ne a madadin jagoran masu fafutukar kafa ƙasar Yarbawa, Farfesa Adebanji Akintoye.
Koiki ya rubuta cewa, “Sunday ya gabatar da ƙarar ne a fadar Downing Street domin ganin ya samun taimakon gwamnatin Birtaniya a fafutukar kafa ƙasar Yarbawa zalla.”
Waɗanda suka rufa masa baya lokacin kai ƙarar gaban Firaiministan na Birtaniya sun haɗa da shugaban matasa mazauna waje, Prophet Ologunoluwa, da Ifeladun Apapo da Fatai Ogunribido da sauransu.