Wani tsohon sojan Amurk ya ce, ya ga yadda sojojin Isra’ila da na ƙungiyar raba kayan agaji ke aikata laifukan yaƙi a Zirin Gaza.
Laftanal Kanal Anthony Aguilar ya tabbatarwa da BBC cewa, ya ajiye aikinsa tare da ƙungiyar Gaza Humanitarian Foundation (GHF), wadda Amurka da Isra’ila ke goyon baya, saboda laifukan da abokan aikinsa ke aikatawa.
“Na yadda sojojin Isra’ila ke harbin dandazon Falasɗinawa,” in ji shi.
Ya ƙara da cewa tun da yake zuwa filin yaƙi a rayuwarsa bai taɓa ganin “irin wannan rashin imani da aikata zalinci a kan fararen hula da ke cikin yunwa ba kamar a Gaza”.