Wani dan takarar gwamnan jihar Ribas, Farah Dagogo, wanda a ranar Larabar da ta gabata cewa, gwamnan jihar, Nyesom Wike ya bayyana yana neman sa ruwa a jallo, ya yi kira ga jama’a da su tuhumi gwamnan idan wani abu ya same shi.
Dagogo, wanda kuma dan majalisar wakilai ne, a jiya ne Gwamna Wike ya bayyana cewa, yana neman sa ruwa a jallo bisa zarginsa da daukar ‘yan kungiyar asiri domin kawo cikas wajen tantance masu neman tsayawa takara a sakatariyar jam’iyyar ta jihar da ke Fatakwal.
A wata sanarwa da mai taimaka masa kan harkokin yada labarai, Ibrahim Lawal ya fitar ranar Alhamis, dan majalisar ya zargi gwamnan da yin karya a kansa.
Ya bayyana cewa bai taba zama a sakatariyar jam’iyyar domin tantancewa ba, kasancewar shi dan takarar gwamna ne ba dan majalisar jiha ko dan majalisar wakilai ba, wadanda aka shirya tantance su ranar Laraba a sakatariyar jam’iyyar.
Da yake bayyana abin da ya faru a wurin tantancewar, dan majalisar ya ce, “da misalin karfe 3:00 na rana, wasu daga cikin masu neman takarar ba su ji dadin yadda a wancan lokacin kwamitin tantancewar ba ya zo da manufar da aka nufa da su.