Shugaban Amurka Joe Biden ya ce ba shi da ƙwarin gwiwar cewa za a samu sauyin shugabanci cikin lumana idan har Donald Trump ya faɗi zaɓen shugaban ƙasar na watan Nuwamba.
A hirarsa ta farko tun bayan da ya janye daga takarar, Mista Biden ya shaida wa kafar yada labarai ta CBS cewa bai kamata a manta barazanar da ɗan takarar Republican ɗin ya yi ba cewa sai an zubar da jini.
Biden ya ce da gaske yake abin da ya fada, kada mu dauka wasa ne.
Shugaban ya kuma ce tsohon shugaban ƙasar, Donald Trump na jam’iyyar hamayya ta Republican zai iya yin koken cewa an yi masa fashi a zaɓen kamar yadda ya yi a 2020.
Yayin da ya rage ƙasa da wata uku a gudanar da zaɓen na Amurka, Donald Trump da Kamala Harris, ‘yar takarar zaɓen ta jam’iyyar Democrat na ƙara zage damtse a yaƙin neman zaɓensu a jihohin da ke zama raba-gardama a zaɓen shugaban na Amurka. In ji BBC.


