Tsohon gwamnan Kano, Injiniya Rabi’u Musa Kwankwaso, ya ce tabbas gwamnatin Kano za ta duba yiwar tsige Sarakunan jihar ko akasin haka.
Kwankwaso ya tabbatar da hakan ne yayin ganawa da manema labarai da ya yi a jihar, tun bayan yanke hukunci da kotun koli ta yi na baiwa jam’iyyar NNPP nasara.
Ya ce dole ne Gwamna Abba Kabir Yusuf, ya duba, idan an daura Sarakunan a daidai za a barsu, idan kuma ba a daidai a ka daura su ba, tabbas za su tube musu rawanin su.
Da aka kuma tambaye shi batun koma wa jam’iyyar APC, ya ce shi kofarsa a bude take muddin za a girmama shi tare da magoya bayansa.


