fidelitybank

Idan PDP ta bukaci mu sasanta TNM ne za su duba batun – Kwankwaso

Date:

Tsohon gwamnan jihar Kano, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso ya ce har yanzu shi ɗan jam’iyyar PDP ne duk da cewa ya soma tattaunawa da jam’iyyar NNPP domin sauya sheka zuwa can.

A hirarsa da BBC, jagoran kungiyar siyasa ta Kwankwasiyya ya ce a makwannin da suka gabata ne suka kaddamar da wata sabuwar kungiya mai suna ‘The National Movement’, bayan nan ne aka samar da jam’iyyar NNPP wato New Nigeria People Party ma’ana dai sabuwar Najeriya.

Kwankwaso ya ce, wannan sabuwar jam’iyya ce ta mutanen da suka amince cewa akwai bukatar tsarin da aka taho da shi daga shekarar 1999 a sauya shi a kawo abin da jama’a za su amfana.

Ya ce, akwai bukatar nazari kan abin da kasa za ta sauya sannan ta samu sabon alkibla, sai dai yana mai jaddada cewa har yanzu ya na nan a cikin jam’iyyar PDP bai fita daga cikinta ba.

”A yanzu maganar da ake yi ina cikin jam’iyyar PDP, tun wancan lokacin mun fara abin hawa-hawa. Abu na farko da muka fara yi shi ne ja baya daga tsarin ta, tunanin wasu masu hankali za su zo a zauna a fada musu abin da ya dame mu amma jam’iyya ba ta yi ba, muka shiga kungiya nan ma ba a yi komai ba, to gamu a matakin jam’iyya. Har yanzu da na ke magana da kai muna tsakanin kungiya da jam’iyya sannan ban fita daga cikin jam’iyyar PDP ba, kuma wannan kungiya ta hade ne da jam’iyyar NNPP. Duk ranar da zan bar PDP ku ne na farko a za ku sani saboda abubuwan ne a tsare su ke mu na komai cikin tsanaki.”

Kwankwaso ya ce, ba wai ya raba kafa ba ne tsakanin jam’iyyar NNPP da PDP kuma idan manyan jam’iyyar PDP suka bukaci a sasanta tsakaninsu ya ce, yanayin zai danganta da abin da suka fada da kuma yadda su sauran abokan tafiya suka kalli lamarin.

”Maganar ba ta Rabi’u Kwankwaso ko ta Kwankwasiyya ba ce, magana ce ta ‘The National Movement’ kuma muna da yawa a ciki, sannan yawancin wadanda ke cikin ta manyan mutane ne dan haka ba zan yanke hukunci ni kaɗai ba.”

Da aka tambaye tsohon gwamnan kan rahotanni da ke cewa an rushe shugabancin jam’iyyar NNPP tun ma kafin su shige ta da kuma kakkabe duk wanda ba ɗan Kwankwasiyya ba da yin sabon zubi da ‘yan Kwankwasiyya sai ya kada baki ya ce:

”A’a ai jam’iyyar daman ba ta mu ba ce, amma ana son mu zo a tafi tare dan haka su na son mu kawo namu su ma su kawo nasu. Sannan lokacin shugabancinsu ya wuce don haka kowa ya sauka, ciki har da shugaban da ya yi mata rijista sama da shekara 20 da ta wuce. Dan haka tsari ne ake hadawa da namu da nasu saboda mafi yawan jihohi ba su da kowa,” in ji Kwankwaso.

nigeria legit news

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Zan cigaba da sa yawan jini ga maƙiya Tinubu – Wike

Ministan Babban Birnin Tarayya, Nyesom Wike, ya sha alwashin...

Tinubu zai magantu a kan ranar Dimokradiyya

Shugaban Kasa, Bola Ahmed Tinubu, zai yi jawabi ga...

A shirye nake na mutu don nasarar APC a 2027 – Orji Kalu

Sanatan Abia ta Arewa, Orji Uzor Kalu, ya bayyana...

Bayan hutun Sallah Tinubu zai koma Abuja

Shugaban ƙasa, Bola Tinubu na kan hanyarsa ta komawa...

Mutane 570 aka kashe a Najeriya cikin watan Afrilu – Rahoto

Hukumar kare haƙƙin ɗan'adam a Najeriya ta ce, adadin...

PDP ba za ta mutu ba duk da rikicin cikin gida – Wike

Ministan babban birnin tarayya Abuja, Nyesom Wike ya ce...

Sojoji sun kashe riƙaƙen ɗan bindiga Guddel a Kaduna

Sojoji sun yi nasarar kawar da fitaccen shugaban ‘yan...

Fadar shugaban ƙasa ta yi kakkausar gargaɗi a kan Ndume

Fadar shugaban kasa ta yi kakkausar gargadi ga dan...

Kare Ya Kashe Ragon Layya: Mai ƙwacen waya ya kashe Sojin ruwa a Kaduna

Wani mai ƙwacen waya ya kashe wani soja bayan...

Sojoji sun hallaka ƴan Boko Haram da dama

Da sanyin safiyar ranar Litinin, dakarun rundunar Haɗin kai...

Tarzomar kama baƙin haure a Amurka na yamutsa hazo

An shiga rana ta uku a tarzomar da ake...

Alhazai sun kammala aikin Hajji bana

A ranar Lahadin da ta gabata ne alhazai miliyan...
X whatsapp