Tsohon gwamnan jihar Plateau kuma jigo a jam’iyyar PDP a jihar, Sanata Jonàh Dàvid Jang, ya yi gargadin cewa, a yayin da zabukan shekarar 2023 ke gabatowa tare da kammala tsare-tsaren da suka kai ga fitar da ‘yan takarar babbar jam’iyyar sa ta PDP, ya bayyana cewa, dole ne su gaggauta hade kai idan ba haka ba su sha kayi a zaben 2023.
Jang wanda ya ba da wannan nasihar a sansaninsa da ke gundumar Due a karamar hukumar Jos ta Kudu a jihar Filato a ranar Juma’ar yayin da yake zantawa da manema labarai cewa, sakamakon zaben gwamnan jihar Ekiti ya nuna cewa, ba za su iya zuwa babban zaben kasar ba tare da raba gidan ba.
“Yana da kyau mu koma kan allo, mu yanke shawarar da ba daidai ba, sannan mu fara tabbatar da cewa, mun shirya zuwa filin zabe ba tare da wani kaya daga shawarar da muka yanke ba.”
Jang na wannan batun ne a lokacin da rikici ke kara tsamari tsakanin Atiku Abubakar da Nyemson Wike.