Tsohon ministan sufurin jiragen sama na jamhuriya na farko, Cif Mbazulike Amaechi, dan shekaru 93 da haihuwa, ya ce, idan saboda wani dalili dan takarar jam’iyyar Labour Party (LP), Peter Obi, ya sha kaye a zaben shugaban kasa na shekara mai zuwa to Najeriya za ta sha wahala.
Basaraken ya bayyana haka ne, a karshen mako, a gidan sa, a wata zantawa da ya yi da zababbun ‘yan jarida yayin da yake bayyana goyon bayan sa ga Obi da abokin takararsa, Datti Baba Ahmed.
Ya yi gargadin cewa, babu wani abu da zai faru da Obi gabanin babban zaben 2023, inda ya bayyana cewa al’amarin Najeriya zai kara tabarbarewa idan wani abu ya same shi (Obi).
Ya ce, “Bana tsammanin hatsari ne kawai Peter Obi ya fito. Ina tsammanin hanyar Allah ce. Idan wani abu ya same shi, zai kara tabarbare al’amura a Najeriya kuma lamarin zai iya rikidewa zuwa wani abu da ba a iya misalta shi ba.
“Idan suna tsoron Obi wanda shi ne mafari, me ya sa ba za su ji tsoro na har abada ba? Peter Obi ne kadai gwamna da ya bar mulki kuma babu wanda ya yi masa wata tambaya.
“Bai san ofishin EFCC, ICPC ko DSS ba saboda tsaftataccen bayanansa. Mutumin da ya gaje shi ya so ya bar kasar sa’o’i biyu da ya mika, ma’ana yana so ya lallace.
“Sauran gwamnoni da dama da suka bar mulki an kama su an gurfanar da su a gaban kotu amma sun shiga majalisar dattawa ko APC a jam’iyya kuma yau an rufe shari’arsu. Irin ruɓar ƙasar da kuke da ita ke nan. Duk da haka mutane suna shan wahala, kuma suna iya ci gaba da shan wahala.
“Ba na jin Allah ya halicce mu don mu ci gaba da shan wahala. Zaben 2023 wata dama ce da ya ba mu domin mu gyara kura-kuran. Za ku ga yadda duk duniya za ta rungumi Najeriya idan Peter Obi ya ci zabe kuma duk masu aikata laifuka da wawaye za su narke zuwa Dubai.”