Tsohon shugaban majalisar dattawa, Bukola Saraki ya bayyana fargabar cewa idan dan takarar shugaban kasa na jamâiyyar Labour, Peter Obi ya zama shugaban kasa a 2023, gwamnatinsa za ta kasance cikin annoba.
Tsohon dan majalisar wanda ya bayyana hakan a wata hira da ya yi da gidan talabijin na Arise a ranar Litinin din da ta gabata, ya ce jamâiyyar Labour ba ta da âyan takarar da za su cika kujerun âyan majalisar dokoki, wanda a cewarsa ba zai yi kyau ba idan jamâiyyar ta lashe zaben shugaban kasa.
Saraki, tsohon gwamnan jihar Kwara, ya ce idan aka zabi Obi a matsayin shugaban kasa ba tare da samun rinjaye a majalisar dokokin kasar ba, dangantakar dake tsakanin bangarorin biyu na iya shafar shugabanci na gari.
Ya ce, âKar ku manta a Najeriya, muna gudanar da tsarin gwamnati na shugaban kasa. Idan ka je akwatin zabe a ranar zabe, kana zaben jamâiyya ne.
“Jam’iyyar da daga rana ta 1, ba ku da ‘yan takara na kujerun majalisa, dama an riga an shirya bala’i saboda kun san cewa zartarwa da majalisa ba za su sami rinjaye ba”.