fidelitybank

Idan na zama shugaba zan haɗa kai da Afrika ta Kudu – Atiku

Date:

Dan takarar shugabancin kasar nan na PDP a zaben 2023, Atiku Abubakar, ya karbi bakuncin Jakadan Afrika ta Kudu a Najeriya, Thamsanga Dennis Mseleku a gidan sa dake Asokoro.

Sanarwar mai kunshe da sa hannun Abdulrasheed Shehu, ya ce, tattaunawar ta su a yayin zaman ta mayar da hankali ne kan yadda za a fadada dangantakar difulomasiyya tsakanin Najeriya da Afrika ta Kudu, domin ya zama sanadiyyar karfafa dangantaka tsakanin kasashen Afrika da nufin samar da tsarin da ake bukata na gina hadin kai da tattalin arziki a Nahiyar.

Dennis Mseleku ya ce, Najeriya na bukatar Mika mulki cikin ruwan sanyi, inda ya yi alkawarin goyon baya daga kasar sa domin Najeriya ta samu gudanar da ingantaccen zabe a 2023. Ya yabawa kasashen biyu bisa yunkurin su na sake karfafa alaka, yana mai cewa abinda kasashen biyu suka fi bukata a yanzu shi ne aiki a zahiri domin inganta tattalin arziki.

A nasa bangaren, dan takarar shugabancin kasar na PDP, ya godewa Jakadan na Afrika ta Kudu bisa ziyarar, inda ya jinjina masa bisa kokarin kyautata alaka tsakanin Najeriya da kasar sa. Wazirin Adamawa ya kuma Yi alkawarin muddin an zabe shi shugaban kasa a 2023, zai yi aiki domin habaka dangantakar kasashen biyu domin saura su yi koyi.

Abdulrasheed Shehu
Mataimaki na Musamman ga Mai girma Atiku Abubakar kan kafafen yada labarai.

29 ga Yuli 2022.

nnn hausa

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Ƴan Jagaliya sun caka wa Matashi kuwa lokacin da ya zo karɓar naman Sallah a Kano

Matashi Ibrahim Mahmud ya rasu sakamakon caka masa wuƙa...

Kallo Ya Koma Sama: Elon Musk zai fuskanci mummunar sakamako – Trump

Ana ci gaba da takun saka tsakanin shugaban Amurka...

Zulum ya miƙa kyautar Naira miliyan 100 ga iyalan Sojojin da aka kashe

Gwamna Babagana Umara Zulum na jihar Borno, ya bai...

Otal ɗin ƴan Najeriya ya kama da wuta wani ɓangaren a Saudiyya

Hukumar Alhazai ta Najeriya ta ce an samu tashin...

An kai hari maɓoyar Boko Haram a Borno

Biyo bayan sahihan bayanan sirri da aka samu, rundunar...

Alaƙar Trump da Elon Musk ta yi tsami sosai

Attajirin da ya fi kowa arziki a duniya, Elon...

An yi jana’izar Muhammad Uwais

An gudanar da jana'izar tsohon alkalin alkalan Najeriya, mai...

Musulman Nijeriya a cigaba da jajircewa – Obi

Ɗan takarar shugaban ƙasa a karkarshin jam'iyyar Labour a...

Akwai takaici ambaliyar Neja – IBB

Tsohon shugaban ƙasa, Janar Ibrahim Babangida, ya kwatanta ambaliyar...

Farfesa Jibril Aminu ya rasu ya na da shekaru 86

Allah ya yi wa Farfesa Jibril Aminu mai shekara...

Alhajin Najeriya ya rasu a tsayuwar Arfa

Wani Alhaji daga Najeriya ya rasu a filin Arfa...

Alhazai miliyan 1.673,230 ne ke gudanar da akin Hajji – GASTAT

Hukumar tattara alƙaluma ta Saudiyya (GASTAT) ta ce, Alhazai...
X whatsapp