Dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar Action Alliance (AA), Manjo Hamza Al-Mustapha (mai ritaya), ya ce, yana son ya zama shugaban kasa a shekarar 2023, domin sake mayar da kasar turbar gaskiya.
Shugaban tsaron marigayi Janar Sani Abacha, Manjo Hamza Al-Mustapha (mai ritaya), ya tabbatar da cewa, alkalumma daban-daban sun nuna cewa, kasar nan na ci gaba da rugujewa, tun bayan hawan gwamnatin Muhammadu Buhari mulki a shekarar 2015.
Al-Mustapha ya yi ikirarin cewa, kishinsa da kaunarsa ga Najeriya ne ya sa ya sake tsayawa takarar shugaban kasa a 2023, bayan wasu kiraye-kirayen da ‘yan Najeriya suka yi.
Ya bayyana hakan ne a ranar Juma’a lokacin da ya fito a matsayin bako a gidan talabijin na Channels.
Al-Mustapha, ya ce, bai shiga takarar shugaban kasa don neman kudi ba kamar yadda wasu za su yi tunani.
Ya ce: “Na yanke shawarar a wannan karon na amsa kiran da yawa daga cikin dattawan Najeriya da matasa daga Arewa zuwa Kudu da kuma wasu makusanta da yawa da na yi aiki da su, na amince da wannan kira na in tsaya takara.