Dan wasan gaba na Liverpool, Mohamed Salah, ya ki yin karin bayani kan karawar da suka yi da kociyan kungiyar Jurgen Klopp, a lokacin da suka tashi 2-2 da West Ham.
An ajiye Salah ne a wasan da aka yi a filin wasa na Olympic, yayin da Reds ke neman dawowa daga kashin da suka yi a hannun Everton da ci 2-0.
Duk da haka, sun jagoranci 2-1 a kan Hammers, lokacin da Klopp ya zaɓi ya kawo shi tare da Darwin Nunez.
Amma yayin da suke jira a kan layi don hutu a wasan, Michail Antonio ya kai wasan 2-2.
Sai dai Salah ya shiga zazzafar muhawara da Klopp wanda hakan yasa Nunez ya ja da baya.
Bayan wasan an tambayi Salah game da lamarin, sai ya amsa da cewa: “Idan na yi magana a yau, za a yi wuta.”