Shahararren dan wasan kungiyar kwallon kafa ta Paris Saint-Germain, Kylian Mbappe, zai samu karin alawus da albashi idan ya ci gaba da zama a kungiyar a kakar wasa ta bana.
Mbappe na iya kan hanyarsa ta barin kungiyar a wannan bazarar, amma yana shirin sanya makudan kudi idan ya ci gaba da zama.
An cire tsohon dan wasan gaban Monaco daga tawagar Luis Enrique don rangadin da suka yi a Japan, wanda ke kara rura wutar rahotannin ficewa.
Kwantiragin dan wasan mai shekaru 24 a Parc des Princes zai kare ne a shekarar 2024 tare da zabin tsawaita zamansa na tsawon shekara daya, amma ya shaida wa PSG cewa ba ya da niyyar tsawaita zamansa bayan bazara mai zuwa.
Mbappe ya rattaba hannu kan kwantiragin shekaru uku a lokacin bazarar 2022 wanda ya yi masa alkawarin ba shi kyautar Yuro miliyan 180, da albashi mai tsoka na Yuro miliyan 630 a tsawon shekaru uku da kuma ikon yin magana kan yanke shawarar canja wuri a kulob din.
Amma makomarsa ta sake shiga cikin kokwanto yayin da masanin musayar ‘yan wasa Fabrizio Romano ya ce ana sayar da kyaftin din tawagar Faransa a hukumance.
Yanzu haka PSG ta bude don siyar da shi, amma za ta iya samun arziki ta zama a kulob din babban birnin Faransa.
Da farko dai, zai iya karbar wani albashin Yuro miliyan 72, fiye da kowane dan wasa a Turai, sai kuma kaso na biyu na kudin sayan, wato Yuro miliyan 60.
Haka kuma, Mbappe zai kuma sami kyautar aminci ta Euro miliyan 90, wanda duk ya kai sama da Yuro miliyan 200. A cewar dan jaridar Faransa Bleu Paris, Romain Beddouk.