fidelitybank

Idan Jonathan ya dawo APC zan yi ritaya daga siyasa – Vatsa

Date:

Jigon jam’iyyar APC a jihar Neja, Mista Jonathan Vatsa, ya sha alwashin ficewa daga jam’iyyar APC da harkokin siyasa, idan tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan ya amince ya tsaya takarar shugaban kasa a shekarar 2023 a karkashin jam’iyya mai mulki.

Ya ce tun a shekarar 2015 jam’iyyar APC mai mulki ta ci gaba da zargin Jonathan da jam’iyyar PDP a kan kalubalen da kasar ke fuskanta, amma yanzu suna shirin mayar masa da mulki.

Vatsa, tsohon kwamishinan yada labarai, al’adu da yawon bude ido na jihar Neja, ya ce idan Jonathan ya amince da matakin, zai amince da kalaman da wani tsohon gwamna ya yi cewa babu da’a a siyasa.

A cewarsa, “Ina addu’ar jita-jita ce kawai ko kuma labarin karya, amma idan tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan ya amince ya tsaya takara a zabe mai zuwa kuma a karkashin jam’iyyar APC, to zan yarda da wani tsohon gwamna da ya taba cewa babu da’a a siyasa. Ba kawai zan bar jam’iyyar ba, zan bar siyasa in koma gona”.

Da yake mayar da martani ga labarin Jonathan ya fito takarar shugaban kasa a karkashin jam’iyyar APC, tsohon sakataren yada labaran jam’iyyar na jihar, ya ce yana sane da cewa jam’iyyar APC na da burin kada ta bar mulki ya koma jam’iyyar adawa ta PDP a 2023.

bbc news nigeria today live

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp