Shugaban Æ™ungiyar ma’aikatan man fetur da gas a Najeriya, Festus Osifo, ya ce har yanzu gwamantin tarayya na biyan kudin tallafin man fetur.
Shugaban na PENGASSAN ya bayyana haka ne a lokacin wata tattaunawa da gidan talabijin na Channels a yau Juma’a.
“Maganar gaskiya ita ce har yanzu akwai tallafi, saboda lokacin da aka yanke farashin fetur, farashin É—anyen man fetur na a dala 80 kan kowace ganga. Amma a yau, farashin ganga guda ya kai dala 94. To saboda ya tashi shi ma farashin fetur dole ya tashi,” In ji shugaban PENGASSAN.
Ya ce kafin gwamnati ta iya janye tallafi gaba É—aya, to dole abu guda biyu su faru.
“Dalilin da zai sanya farashin fetur ya daina tashi sai dai idan Najeriya ta iya daidaita darajar kudinta da na Æ™asashen waje,” In ji Osifo.
“To idan har farashin kudaden Æ™asashen waje ya sauko a yau, to ba zamu ci gaba da biyan tallafi ba.
Amman saboda yanayin farashin danye mai a kasuwar duniya da kuma faduwar darajar Naira ya sanya dole muka gabatar da tallafi.”
Gwamnatin Najeriya ta kwashe gwamman shekaru tana biyan maƙudan kuɗaɗe a matsayin tallafin man fetur, lamarin da ya taimaka wajen sauko da farashin fetur a Najeriya.