Tsohon dan wasan kungiyar kwallon kafa ta Arsenal, Thierry Henry, ya ce ba zai taba yiwuwa a ce ba a sno Manchester City ba.
Henry ya bayyana haka ne a gidan rediyon CBS, bayan da City ta doke Real Madrid da ci 4-0 a daren Laraba, inda ta samu gurbin shiga gasar cin kofin zakarun Turai da ci 5-1 a jimillar.
Mutanen Pep Guardiola yanzu suna gab da samun nasarar lashe Kofin da ba a taba ganin irinsa ba.
City za ta iya lashe gasar Premier a karshen wannan mako da Chelsea, yayin da za ta kara da Manchester United a wasan karshe na cin kofin FA.
Sun kare kakarsu da wasan karshe na gasar zakarun Turai da Inter Milan a ranar 10 ga watan Yuni.
Henry ya ce: “Kowa ya san ni masoyin Arsenal ne, amma idan ba kwa son Man City, tabbas kuna da matsala a kan ku.”