Gwamna Seyi Makinde na jihar Oyo ya ce, mafita daya tilo daga cikin rashin fahimtar juna a jam’iyyar PDP shi ne shugaban jam’iyyar na kasa, Sanata Iyorcha Ayu ya yi murabus.
Makinde ya bayyana hakan ne a ranar Laraba a Ibadan.
Ya yi wannan jawabi ne a wata tattaunawa da dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar PDP a zabe mai zuwa na 2023, Abubakar Atiku da jiga-jigan jam’iyyar daga shiyyar Kudu maso Yamma.
DAILY POST ta rahoto cewa Atiku ya isa Ibadan ne tare da gwamnoni Ifeanyi Okowa na jihar Delta, da abokin takararsa, Aminu Tambuwal na Sokoto, Sanata Ademola Adeleke, Soji Adagunodo da Cif Raymond Dokpesi.
Sauran sun hada da tsohon gwamnan jihar Neja, Babangida Aliyu da takwarorinsa na Ondo, Olusegun Mimiko da Osun, Olagunsoye Oyinlola, Eyitayo Jegede, Dino Melaye da Ladi Adebutu.
Gwamna Seyi Makinde na jihar Oyo da mataimakinsa Adebayo Lawal da kakakin majalisar dokokin jihar ne suka tarbi shugabannin PDP.
Makinde ya bayyana cewa dole ne jam’iyyar PDP ta gyara kanta kafin ta sake fasalin Najeriya.
Ya ce daya daga cikin sharuddan sake fasalin jam’iyyar shi ne Ayu ya yi murabus, yana mai bayanin cewa dan takarar shugaban kasa, Atiku dan Arewa ne yayin da Ayu kuma dan Arewa ne.