Mataimakin shugaban kasa Kashim Shettima, ya yi kira ga ‘yan Najeriya da su rungumi juna domin fatattakar talauci da fatara a kasar nan.
Shettima ya bayar da shawarar ne a garin Masaka na jihar Nasarawa a ranar Alhamis, yayin da yake kaddamar da hanyar Masaka zuwa Luvu mai tsawon kilomita 5 a karamar hukumar Karu ta jihar.
Mataimakin shugaban kasa, Kashim Shettima, ya kuma jaddada bukatar dukkan ‘yan kasa su koyi zama tare da juna cikin lumana domin bunkasa tsaro domin ciyar da kasa gaba.
A cewarsa, ba za a taba samun wani ci gaba mai daurewa ba, idan ba zaman lafiya ga juna.
Shettima, wanda shi ne babban bako na musamman a wajen taron, ya yi amfani da wannan damar wajen yaba wa Gwamna Abdullahi Sule na Nasarawa bisa yadda yake wanzar da zaman lafiya a yankinsa.


