Jagoran addini na Iran, Ayatollah Ali Khamenei ya ce babu abin da barazanar Amurka za ta yi ma ƙasarsa.
A cikin jawabin da ya gabatar na murnar zagayowar sabuwar shekarar Farisa, ya ce Amurka za ta ɗanɗana kuɗarta idan har ta ɗauki wani mataki kan Iran.
Ya ce ya kamata Amurka ta sani cewa barazanar da take na yin gaba-da-gaba da Iran ba zai zo mata da sauƙi ba.
Khamenei ya ce dukkansu ya kamata su sani cewa idan suka taƙali Iran to za su gane ba su da wayau.
Tun a farkon wannan watan ne Ayatollah ya yi watsi da takardar da shugaban Amurka ya aika masa ta neman tattaunawa kan shirin Iran din na Nukiliya.