fidelitybank

Idan aka haramta TikTok sama da miliyan 170 za su rasa aikin yi a Amurka – TikTok

Date:

Shugaban shafin sada zumunta da muhawara na TikTok ya ce, kamfanin zai yi duk abin da zai iya domin kare kansa, bayan da majalisar wakilan Amurka ta amince da wani ƙudurin doka, da zai iya kaiwa ga haramta amfani da shafin a Amurka.

Fadar Gwamnatin Amurka, White House, ta yi kira ga ‘yan majalisar dattawa da su gaggauta amincewa da ƙudurin, wanda ‘yan majalisa suka ce zai kare Amurkawa daga barazanar alakar TikTok ɗin da gwamnatin China.

A wani bidiyo da ya sanya a shafin na TikTok, shugaban kamfanin Shou Zi Chew ya yi gargaɗin cewa muddin aka zartar da wannan doka, to dokar za ta kai ga hana amfani da shafin gaba ɗaya a Amurka.

A don haka ya ce, kamfanin zai yi amfani da dama da ƴancin da yake da shi na doka ya kare shafin da kuma Amurkawa miliyan 170 da suke amfani da shi.

Mista Chew ya ce manufar matakin kawai haramta amfani da manhajar ne.

Ya ce: ”Wannan dokar, idan aka amince da ita za ta kai ga hana amfani da TikTok ne a Amurka. Hatta ma waɗanda suka kawo ƙudurin sun yadda cewa burinsu ke nan. Wannan ƙudurin doka ya bayar da ƙarin iko ga wasu kamfanonin shafukan sada zumunta da muhawara ƴan kaɗan. Haka kuma zai raba masu ƙirƙira da masu ƙananan harkokin kasuwanci biliyoyin dala. Zai kuma jefa aikin Amurkawa sama da dubu 300 cikin ha dari, kuma zai ɗauke TikTok dinku.”

Fadar gwamnatin Amurka, White House ta ce tana goyon bayan ƙudurin dokar, da zai bai wa masu shafin ƴan China damar kusan wata shida ta ko dai su sayar da shafin ko kuma su fuskanci haramcin amfani da shi a wayoyi. In ji BBC.

Ƴan majalisar na ɗaukar shafin a matsayin wata barazana ga tsaron Amurka.

Kamfanin na TikTok ya musanta alaƙa da gwamnatin China, ya kuma buƙaci masu amfani da shafin a Amurka, da su yi ta kiran wayoyin ƴan majalisar, su buƙace su da su yi watsi da wannan doka.

daily post news

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp