fidelitybank

ICPC ta kama mawaki D’Banj kan badakalar N-Power

Date:

Hukumar yaƙi da rashawa ta ICPC ta kasa, ta ce ta kama mawaƙin nan mai suna Oladipo Daniel Oyebanjo, wanda aka fi sani da D’Banj kan wani bincike da take yi wanda ya shafi kuɗaɗen shirin N-Power.

Wata sanarwa da hukumar ta wallafa a shafinta na intanet ta ce ta kama D’Banj ne saboda ya ƙi martaba gayyatar da hukumar ta yi masa game da batun.

Sanarwar ta ce, ta gayyaci kimanin mutum 10 a cikin watannin da suka gabata a kan binciken da take yi game da badaƙala ta kuɗin N-Power, kuma tuni ta sake su, sai dai ta riƙe D’Banj bayan da ya kai kansa babban ofishin hukumar da ke Abuja a ranar Litinin saboda ƙin martaba gayyatar da ta yi masa a baya.

ICPC ta ce, yanzu haka mawaƙin na tsare a ofishinta kuma yana taimakawa a wajen binciken da ake yi.

Ta kuma ce, za ta tabbatar an hukunta duk mutane ko bankuna da suka taimaka wajen badaƙalar.

nnn

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp