Hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta ICPC, a Najeriya ta ce ta fara bincike kan zargin samun shaidar karatun digiri ba bisa ka’ida ba a jami’ar Cotonou da ke jamhuriyar Benin.
ICPC ta bayyana hakan ne a shafinta na intanet, inda ta ce shugaban hukumar Dr. Musa Adamu Aliyu, SAN, ya kira wani taro a kan batun, a ranar Talata.
Binciken zai shafi jami’ar Ecole Superieure de Gestion et de Technologies (ESGT) ta Cotonou wadda ake zargin tana bayar da shaidar digiri a kasa da mako shida.
Hukumar ta ce za ta yi binciken don gano hanyoyin da ake bi domin yin badakalar da zummar kawo gyara a tsarin karatun.
Sannan za ta yi hadin guiwa da hukumomi na cikin gida da na waje domin tabbatar da ingancin shaidar karatun tare da zakulo wadanda ke da hannu a al’amarin.
Rahotan da ya bankado hakan ya yi zargin cewa ana samun kwalin karatun ba tare da bin hanyoyin da suka dace ba, kamar rashin gabatar da takardar bukatar yin karatu da rijista da karatun da kuma rashin rubuta jarrabawa.
Hakan na zuwa ne bayan gwamnatin Najeriyar ta sanar da dakatar da karbar shaidar digiri daga Cotonou da kuma Togo sakamakon badakalar.


