Daya daga cikin manyan Limaman harami, Sheikh Maher Al-Muaiqly, ya jagoranci huɗuba a filin Arfa.
Jaridar Saudi Gazzet ta ce huɗubar malamin ta yi kamanceceniya da huɗubar da Annabi S.A.W ya gabatar a Hajjin Bankwana.
Limamin ya umarci musulman duniya su yi biyayya ga biyayya ga umarnin Allah S.W.T, sannan su kauce wa abin da ya haramta, domin samun tsira da nasara a duniya da lahira.
“Aikin Hajji alama ce ta nuna tsarkake ubangiji a ibada, kuma ba wuri ba ne na ambaton kalaman siyasa,” in ji shi.
“Ya ku mahajjata da ke ziyara a ɗakin Allah, ku yi addu’a ga Ubangiji, ku nemar wa iyayenku da ‘yan uwanku gafarar ubangijinku. Duk wanda ya yi wa ɗan uwansa addu’a a bayan idonsa, mala’iku za su yi masa kwatankwacin addu’ar.” in ji limamin